Wata daliba mai suna Aisha Abdullahi, dake aji hudu a fannin Biochemistry a jami’ar Northwest University dake Kano, ta bayyana cewa yawancin ‘yammatan dake jami’ar suna son aure, amma samarin suna tsoron zuwa wajensu saboda tsoron kada ayi musu zancen aure.
AIsha ta bayyana haka a lokacin wata lakca da kungiyar dalibai ta jami’ar ta hada, wacce aka yiwa take da ‘Kalubalen Aure a Karni na 21’, wanda aka gabatar a ranar Alhamis 20 ga watan Fabrairun nan, a cikin makarantar dake Tudun Yola, Kano.
Tace yawancin samarin yanzu suna zuwa soyayya ne kawai ba wai aure ne yake kawo su ba, hakan ya sanya yawan matan da basu da aure yake kara karuwa a kullum.
Ta bayar da misali da wani saurayi da yayi soyayya da ita na tsawon shekara biyu, amma da ta dauko zancen aure, sai ya gudu.
Haka kuma ta dora laifin hakan da son rayuwa ta karya da muke dorawa kanmu, hakan yasa kullum matsalar rashin aure ke karuwa a cikin matasa.
Da aka tambayeta idan ta shirya yin aure bayan kammala jami’ar ta, ta ce idan har ta samu wanda ya shirya aurenta mai zai hana kuwa.




