Hakan na zuwa ne bayan da kasar Amurka ta dakatar da baiwa ‘yan Najeriya da izinin shiga ‘Visa’ ta masu neman mafaka da ma’aurata.
DABO FM ta tattara cewar a watan Janairu ne aka tsayar da watan Maris a matsayin watan da masoyan biyu zasuyi aure bayan ita baturiyar ta kamalla tanadar takardu domin daurin aure.
Da yake shaidawa Daily Trust, mahaifin Sulaiman, ya bayyana cewar da zarar an sanya sabon lokacin, zai fadawa manema labarai.




