
Tauraron fina-finan Hausa, Ibrahim Maishinku ya saka wata fasta da yayi shida shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda yake nuna goyon bayanshi a gareshi.
Bayan saka waccan fastane Maishinku yace ya samu wasu suna zaginshi duk da cewa yawancin wadanda suka yaba da abinda yayi sunfi yawa. Yace hakan ya kara mai karfin gwiwa akan soyayyar da yake wa shugaba Buharin.
Yace bari ya yiwa mutane tuni da irin halin ni 'yasu da Najeriya ta samu kanta inda har daga kasashen wace aka rika mana hasashen wargajewa musamman ma mu a nan Arewa, yace tabbas Allah ne me kariya amma Buhari ya cecemu daga shirye-shiryen wargaza kasarnan da akayi.
A karahe yayi kira ga mutane su manta da komai su goyi bayan shugaba Buharin ya zarce a 2019.