
NA ‘DAYA.
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki.
NA BIYU.
A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin d’aya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.
NA UKU.
Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya.
NA HU’DU.
Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan, lokaci na shud’ewa soyayyar ki na k’aruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena. Ina k’aunar ki.
NA BIYAR.
SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata.
NA SHIDA.
SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai k’ona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.
NA BAKWAI.
Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada. Na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kud’i.
NA TAKWAS.
Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki.
NA TARA.
Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo nan bada dadewaba domin ki tabbatar da abun da na ke fad’a gaskiyane dama an ce zuwa da kai ya fi sak’o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata. Ina son ki.
NA GOMA.
Abba ne zaune a kan wata farar kujerar roba cikin wani lambu mai d’auke da korayen ciyayi da ni’ima mai dad’i, wajen da ya zamo masa wajen hutawar shi a dukkan lokacin da ya fita wajen aiki bayan ya yi aikin ya gaji nanne inda ya saba zuwa ya kirawo matar shi a waya domin jin halin da ta ke ciki tun bayan auren su wanda hakan ba karamin burge matar tashi yake yi ba sannan kuma yana k’ara soyayyar shi a cikin zuciyarta.
Yauma dai kamar kullum, ya fito da wayar ta shi daga aljihu ya shiga kiranta, kamar jira ta ke yi dama bugu d’aya ta d’aga, bayan sallama sai kuwa ya shiga cewa da ita
“Matata Uwar ‘ya’yana maganin kukana, Salimat a baya kafin mu yi aure na yi tinanin cewa bayan mun yi aure ba zan ke samun kulawa da tarairaya tare da kalaman soyayyar nan ta ki masu dad’i ba, na yi zaton komai zai canja kamar yadda na ke gani a wasu gidajen auren ashe mu ba haka abun ya ke ba saima abun da ya ci gaba ya kuma sauya sabon salo mai dad’i, Salimat ina son ki, koda aiki nake yi yadda zan dawo gida na tarar da ke kawai na ke yin tinani, kuma koda abinci zan ci ina ci ne kawai saboda na rayu amma ba wai dan ina jin dadin shi ba, ina son ki sanar da ni abun da zan taho miki da shi idan zan dawo gida ki kuma kular min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawar ki ta dawo hannuna.
A.M. ‘Dan-Hausa.
#HausaKawai.
KALAMAN SOYAYYA.
(Domin Samari Da ‘Yammata Da Ma’aurata)
MARUBUCI: Abba Muhd ‘Dan-Hausa.
NA SAMARI DA ‘YANMATA.
Na Maza:
KIN ZARCE SAURAN MATA.
Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.
SINADARIN RAYUWA TA.
SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
ZAN SO KI JI.
Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!
KE CE MURMUSHI NA.
Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.
SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.
Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!
HMM!! KI YARDA DA NI.
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.
INA SON KASANCEWA A TARE DA KE HAR ABADA.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.
A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.
Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.
HARSHEN ZUCIYA.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan ta6a canjawa a kan hakan ba.
Na Mata:
INA SONKA MASOYI NA!
Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi na bu’katar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bu’katarka domin na yi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!
MU KASANCE A TARE.
Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka!
INA FATAN MAFARKI NA YA ZAMA GASKIYA.
A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son Ka!
MASOYI NA.
Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa fad’uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.
KA ZAMA RUHI NA.
Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ‘karshe, saboda kai ba saurayi ne kawai a waje na ba, ka zama ruhi na, sonka na yawo ne a cikin jinin da ke gudana a jiki na. Ina Son Ka!
NA MA’AURATA.
Miji:
INA SON KI!
Ba zan iya musalta adadin yadda sonki yake lunkuwa a zuciya ta ba a cikin kowace rana. Ina son ki matata. Babu wani abinci da yake yi min dad’i a baki na matu’kar ba ke kika girka shi ba. Ina nan tafe izuwa gare ki da shirin zuwa cin abincinki mai dad’i. Ki kula min da kanki.
ZUCIYA TA NA CIKE DA KEWARKI MATA TA.
Mata ta uwar ‘ya’ya na. Na kan yi kewarki sosai a dukkan lokacin da na duba gefe na ban gan ki ba. kamar kullum, yanzu haka ina zaune cikin tinaninki. Zuciya ta na cike da kewarki, zan samu sassauci ne kawai idan na ji ki a kusa da ni. Ki kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawarki ta dawo hannu na. Ina Son Ki.
BA NI DA KAMAR KI.
Na futo wajen aiki hakan na nufin mun yi nesa da juna. Amma ina son, ki san da cewa, a duk inda nake, a duk inda na shiga, ba zan rabu da tinaninki a matsayinki na mata ta da nake matu’kar so da ‘kauna ba. Ina nan tafe a hanya zuwa gare ki. Ki kasance mai tina cewa, ba ni da kamar ki. Ina Son Ki.
Mata:
INA ALFAHARI DA SAMUNKA.
Hasken idaniya ta, annurin rai na. Miji na, uban ‘ya’ya na. Tabbas samun miji irinka shi ne abun da mata da yawa suke fata. Na same ka hakan ya sanya nake jin tamkar na fi kowace mace sa’a a duniya. Ina fatan dawowarka gida lafiya, miji na abun alfahari na.
KAI NE NAKE GANI NA JI SANYI A ZUCIYA TA MIJI NA.
Ina fatan kana nan lafiya miji na? Ina nan zaune cikin gida amma zuciya ta tana tare da kai. Kai ne kawai nake gani na ji sanyi a cikinta. Ina nan ina jiran dawowarka gida lafiya. Ina son ka. Ka kula min da kanka.