Wata kotun al’adu da ke birnin Ibadan a ranar Alhamis ta raba wani auren shekaru 3 da ke tsakanin wata mata Temilade Oyeyemin da mijinta, Ayo Oyeyemi, a kan zargin yaudara da zina.
Temilade, ‘yar shekaru 28, ta bayyanawa kotu irin kuncin da mijinta ya saka ta a yayin da bayyana sakadar mijin a matsayin gwaggonsa.
“Bayan na sadaukar da rayuwa ta ga auren da ke tsakani na da mijina, Ayo, na shekaru a shi yana baya na yana cin amana da sadakarsa wacce ta kasance gwaggonsa.
“A lokacin auren mu, ya gabatar da matar ga iyalai a matsayin macen da za ta iya tsayawa a madadin mahaifityarsa marigayiya, sannan iyalan suka amince da yaudararsa.
“Sai Ayo ya dauke ni zuwa gidan masoyiyarsa don yin zaman aure,” ta ce.
Temilade ta ce wannan ta bata duk abunda ta ke bukata sannan ta kasance tana jin dadin zama d masoyan su 2.
“Duk da haka, sai na gano cewa da misalin karfe 1:00 na dare a kusan kowane rana, Ayo ya kan bar dakin aurensa.
“Sai ya koma kwanciya kasa inda masoyiyarsa wacce ya ce gwaggonsa ce ke kwana don su yi jima’i.
“Yawanci ya kan ce zafi ke hana ci kwana bisa kan gado, shi ya sa ya ke kwanciya kasa.
“Daga nan sai na gano cewa Ayo da wannan matar ba su da wani alaka da juna, gaskiyar maganan, masoyiyarsa ceta sirri.”
Temilade ta ce a lokacin da ta ke dauke da juna biyu, Ayo bai kula da ita sai ya bar duk hidimar a bisa kan surukkansa.
“Ayo ba mutumin da za a yarda da shi ba ne, mugun miji ne,” saboda haka ina ne alfarma a raba aure a tsakani na da shi, Temilade ta ce.
Shi mijin wanda ake zargi dan shekaru 38, ya bukaci kotun kada ta raba auren da ke tsakaninsa da matarsa bayan ya karyata zargin da Temilade ta gurfanar da shi a gaban kotu a kai.
Ayo, yayi da’awar cewa shi injiniyar gini ne, inda ya bayyana cewa matarsa ba ta da wani amfani sannan kuma ba ta son yin aiki
“Mai shari’a, ni ke girki da wanke-wanke a gida na; na dade ina kula da bukatun Temilade,” Ayo ya ce.
A lokacin da ya ke bada na sa bayanin ga kotun, mahaifin Ayo, duk da haka, ya bayyana dan na sa a matsayin banzan miji sanna kuma mazinaci.
“Ayo ba fadawa kowa zai yi aure ba sannan kuma abun ya ba mu mamaki a kan yadda abubuwa suka wakana.
“Babu wanda yasan masoyiyarsa wacce ya ke bayyanawa Duniya cewa gwaggonsa ce.
“Gaskiya magana shine, Ayo ba taba kula da ni ba tunda na samu hatsarin mota a shekarar 2010.
“Ina mai yin addu’a kotun za ta iya sulhunta wannan lamarin a tsakaninsu,” mahaifin Ayo ya roka.
Wasu daga cikin iyaylen Temilade a na su bayanin ga kotun sun nuna shaidar yadda Ayo ke cin zarafin matarsa sannan sun roki kotun da ta raba aure a tsakanin ma’auratan.
Alkalin da ke sauraran karar a kotu, Mr. Sulaiman Olaniyi, ya ce, “domin samar da zaman lafiya, ya raba auren da ke tsakanin ma’aurata Temilade da Ayo.
“Temilade za ta ci gaban da rikon dan na su na shekaru 2 da rabe a yayin da Ayo zai rinka biyan kulawa da yaron a wata zai biya mahaifiyar naira N3,000 domin kulawa da dan na su.” NAN ta ruwaito.
Olaniyi, ya ce babu yaudarar da za ta dade har abada ana kitsa ta, sannan kuma ya shawarci maza matasa da su kula da iyayensu domin kada su fuskanci fushin Ubangiji.