Home

Music

Video

Kanny

Manoman Nijeriya Sun Ki Biyan Bashin Biliyan 60 Da Suka Amsa -Bankin Noma





A ranar Laraba ce a Legas, Bankin Manoma (BoA), ya bayyana cewa, a kwannan nan ne zai bullo wa manoman da suka yi taurin basukan da Bankin ya ba su wanda jimlan su ya kai Naira bilyan 60, ta bayan gida.

Babban Manajan Bankin, Mohammed Kabir, ne ya bayyana hakan wajen wani taron karawa juna sani da reshen Bankin da ke Agege ya shirya.
Mista Kabir, wanda manajan shiyyan Kudu maso Yamma na Bankin, Idiat Folorunsho, ya wakilce shi, ya ce, a yanzun haka Bankin ya dukufa ne wajen tallafawa matasan da suke da azamar komawa gona.

“A yanzun haka, muna kan shirin daukan matakan kwato kudaden mu ne, domin kuwa har yanzun kudaden mu Naira bilyan 60 suna waje ba a dawo mana da su ba.
“Idan manomi ya karbi rance, sai ya ki dawowa da rancen, to ta ya ya ne za a iya taimaka wa wasu da suke son su ma a tallafa ma su su yi aikin noman su ciyar da tattalin arzikinmu gaba.

“Muna ma son mu kara bude rassa domin mu kara kusantar da Bankin ga al’umma, amma ta ya ya za mu iya yin hakan, alhalin wadancan makudan kudaden suna hannun mutane.

“Wasu manoman sukan karbi kudin ne, amma ba za mu iya bin su mu karbo ba, saboda sun ma canza wuraren da suke zaune da makamantan hakan,” in ji shi.

“Amma lamarin ba laifi a nan shiyyan Kudu maso Yamma,” in ji shi.

Mista Kabir, ya ce, matsalan yawanci a wajen maza take, amma mata akwai su da kokarin biyan basukan.

Ya kuma ce, kamata ya yi sauran Kananan Hukumomi su yi koyi da Karamar Hukumar ta Kosofe, da ke Jihar Legas, wacce ta baiwa Bankin wajen zama da gidajen kwanan ma’aikata da ma filin da Bankin zai yi ginin shi na dindindin.

Sama da mutane 250 ne suka halarci taron kara wa juna sanin, da suka fito daga Ma’aikatu, cibiyoyin kasuwanci, kamfanoni da kungiyoyin manoma da sauran su.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega