Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen jami'an jam'iyar PDP da ta gwamnatin data shude wadanda suka yi wa arzikin Nijeriya cin zomo ga harawa tare da yawan kudaden da kowannensu ya sata.
Bayan jam'iyar adawa ta PDP ta bukaci a fitar da sunayen wadanda gwamnatin jam'iyar APC mai ci take zargi da laifin wawure kudin jama'a, ministan watasa labarai Lai Muhammed ya fitar da jerin sunayen.
Ga jerin sunayen kamar haka;
1. Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus: Ya karbi miliyan 200 ranar 19 ga watan Fabrairun 2015 daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro (NSA). 2. Tsohon sakataren kudin jam'iyyar PDP: A ranar 24 ga watan Oktoba, 2014, ya karbi miliyan N600m daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa a kan harkar tsaro.
3. Tsohon sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Olisah Metuh: Ana tuhumar sa da karbar biliyan N1.4bn daga ofishin tsohon NSA.
4. Dakta Raymond Dokpesi: Shugaban kamfanin DAAR; mai gidan talabijin na AIT da gidan Radiyon Ray Power. Ana tuhumar sa da karbar biliyan 2.1 daga ofishin tsohon NSA.
5. Tsohon mai bawa tsohon shugaban kasa Jonathan shawara, Dudafa Waripamo-Owei: An gurfanar da shi bisa boye kudi miliyan N830m a asusu daban-daban.
6. Dan uwan tsohon shugaban kasa, Robert Azibaola: An gurfanar da shi gaban kotu ranar Alhamis bisa tuhumar karbar Dala biliyan $40m.
Ministan ya kuma fitar da sauran sunayen wasu da ake ma zargin kawo ma tattalin arzikin kasa cikas inda yace ba su shi ya kirkira sunayen ba domin mafi yawancin su suna gaban kotu inda ake tuhumar su kan laifin da suka aikata kuma wasu daga cikin su suna son kotu ta basu dama su mayar da wani kaso na daga cikin kudaden da suka sata domin kotu ta sake su.
A karo na biyu na jerin sunayen wadanda ake zargi da kuma adadin kudin da suka sata akwai:
1. Tsohon NSA Sambo Dasuki: $2.1bn, N126 billion, $1.5 billion, Fam 5.5 miliyan
2. Tsohon ministan man fetur Diezani Alison-Madueke: N23bn, $3 billion
3. Laftanal Janar Kenneth Minimah: N13.9 billion
4. Laftana Janar Azubuike Iejirika: N4.5 billion
5. Tsohon shugaban soji, Alex Barde: N8billion
Daga: Pulse Nigeria