Home

Music

Video

Kanny

Yadda Na Samu Kubuta A Daren Da Boko Haram Su Kutsa Makarantarmu A Dapci




Wata ‘yar shekara 15 mai suna Amina Malam Usman wacce ta samu kubuta a lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari makarantarsu a garin Dapci ta bayyana yadda ta tsallake rijiya da baya a daren ranar da mayakan suka zo sace mu.

.Da Amina ke zantawa da jaridar The Nation, ta bayyana cewa:
“Lokacin da ‘yan Boko Haram din suka zo makarantarmu mun zaci sojoji ne, saboda sun yi shiga irin ta sojoji. Sai muka sheka a guje,sai daya daga cikinsu ya kira mu. Sai wani daga cikinsu ya ce inzo kusa da motar.
“Lokacin da na zo kusa da motar, sai daya daga cikinsu ya fara yi mini dariya, na kara matsawa kusa da su, ina zaton sojoji ne.
“Daga nan sai jikina ya ba ni cewar wadannan ba sojoji bane, sai na yi kokarin shekawa a guje inda wani daga cikinsu ya yi kokarin kama ni sai na subule masa amma ya samu ya janye hijabi na.
“Sai na yi sauri na subule hijabin na bar masa na runtuma a guje. Na yi tsammanin na mutu.

“Sai suka shiga dakunan kwananmu na dalibai, amma tuni wasu sun runtuma da guda cikin jeji. Na yi gudun fitar rai na akalla kilomita 5 inda na tarar da wani kauyen Fulani da ake kira Miligiya na buya a nan”
Lokacin da aka tambayi Amina ko za ta iya tuna ko dalibai nawa ta gani a cikin motar wadanda suka zo yin garkuwa da su sai ta ce: “Gaskiya suna da yawa domin akalla wadanda na gani a cikin motar a lokacin za su kai kimanin 50”

Ta ce a lokacin ji tayi ina ma a ce mala’ikan mutuwa ya zare ranta a lokacin da ta fahimci cewar wadannan mutanen ‘yan Boko Haram ne.
Ta ce ita a yanzu gaskiya ba tajin za ta iya sake komawa wannnan makarantar ta su dake Dapchi.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega