
Jaridar The Nation ta rawaito cewa wani likita dake cibiyar lafiya ta federal medical center dake garin Bida a jihar Niger ya yi sanadiyyar rasuwar wata ‘yar shekaru 16 mai suna Fatima bayan ya dirka mata ciki a yayin da take jinyar mahaifiyarta a asibitin
Rahoton ya bayyana cewa likitan mai suna Dakta Seyi ya yi ta cin zarafin Fatima a ofishinsa bayan ya kira ta da sunan bayyana mata wasu abubuwa game da rashin lafiyar mahaifiyarta dake fama da matsanancin ciwon siga.
Likitan ya yi ta amfani da damar jinyar mahaifiyar Fatima yana lalata da ita har ta kai ga daukar juna biyu kamar yadda wasu ‘yan uwan Fatima da suka nemi a sakaya sunansu suka bayyana
‘Yan uwan sun bayyana abin takaici da halin la hau lan da Fatima ta tsinci kanta kafin rasuwarta inda suka ce
“A yayin da muka tabbatar Fatima na dauke da juna biyu ne muka bukaci ta fada mana wanda ya yi mata ciki kuma ta bayyana mana cewa likitan dake kiwon lafiyar mahaifiyarta ne ya yi mata ciki”
“Liktan ya musanta kusantar Fatima a lokacin da aka tuhume shi lamarin da ya tsananta har muka kai shi gaban sarkin garin Bida. Anan ne ya amsa rungumar Fatima ba tare da ya kwanta da ita ba”
Fatima dai ta hakikance lallai likitan ne ya yi mata ciki ta hanyar kwanciya da ita da karfin tsiya a lokacin da take jinyar mahaifiyarta har ta samu sauki suka koma gida
Sarkin Bida, Alhaji Abubakar Yahaya ya umurci a gudanar da gwajin tabbatar da gaskiyar lamarin (DNA) sai dai Fatima ta rasa ranta ne kafin sakamakon wannan gwajin ya fito bayan ta haifi ‘da na miji.
Hukumar kare hakkin kananan yara ta jihar Neja karkashin jagorancin darakta janar na hukumar ta ce za ta cigaba da bibiyar al’amarin a yayin da suke jiran sakamakon gwajin da shan alwashin gurfanar da likitan idan aka same shi da laifi.