Wata dalibar jami'a ta hadu da ibtila'i inda ake zargin wasu sun watsa mata ruwan guba a garin Maiduguri na jihar Borno na arewa maso gabashin Najeriya.
Fatima Habu Usman, wacce daliba ce da ke karatu a sashen koyon aikin jinya a jami'ar Maiduguri, tana cikin mayuwacin hali yanzu haka.
Wasu mutum biyu ne ake zargi sun watsa ma ta ruwan guba na Acid bayan ta shiga Keke Napep ko a daidaita sahu a ranar Juma'a.
Wani malamin jami'ar ta Maiduguri ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin, yayin rahotanni suka ce 'yan sanda sun kaddamar da bincike.
Birnin ya sha fama da hare-haren kungiyar Boko Haram, amma ba a sa ran cewa su ne suka aikata wannan aika-aikar.
Dangin dalibar sun shaida wa kafar yada labarai ta
PRNigeria cewa, an sace ta ne a gaban wani banki da ta je domin cirar kudi.
Suka ce bayan ta shiga Keke Napep a hanyar Baga ne, ba ta sani ba, sai daya daga cikin mutanen da ke ciki ya fitar da wani kyalle fari ya shafa ma ta a fuska.
Daga nan ne ta fita hayyacinta, kuma sai ta tsinci kanta a kan kwangirin jirgin unguwar Bayan Quarters a Maiduguri misalin karfe daya na rana, kuma an yi ma ta lahani da ruwan guba a jikinta.
Dalibar dai tana shekarar karshe ne a jami'a.
Yanzu haka likitoci na gudanar da gwaje-gwaje a kan Fatima tare da duba yiyuwar ko za a yi mata tiyata a fuska.
PRNigeria ta ambato kwamishinan 'yan sandan na jihar Borno, Damien Chukwu, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa suna gudanar da bincike domin gano wadanda aikata lamarin.