Home

Music

Video

Kanny

Ka Ji Tsoron Haduwarka Da Allah, Shi Kadai Ya San Yawan Mutanen Da Ke Kwana Da Yunwa A Mulkin Ka - Nasihar Ummi Zeezee Ga Buhari



Ka Ji Tsoron Haduwarka Da Allah, Shi Kadai Ya San Yawan Mutanen Da Ke Kwana Da Yunwa A Mulkin Ka - Nasihar Ummi Zeezee Ga Buhari
Amma ku da ya ke jahilan addini ne bayan sa kuke bi

"Ai ba karya na fada ba gaskiya na fada cewar, ya jefa kasa yunwa da talauci da fatara, amma tsoro ya hana a yi magana a ba shi shawara ko zai canja. To ya ji tsoron haduwarsa da Allah, domin Allah kadai ya san yawan mutanen da ke kwana da yunwa a dalilin mulkin sa. Kuma hakkin duk yana wuyansa ran Kiyama sai Allah Ya tuhume shi, don kuwa hakkin kowane dan kasa a wuyansa ya ke.
Amma ku da ya ke jahilan addini ne bayan sa kuke bi. Amma cikin masoyan nasa masu ilimin addini in an zage shi shiru suke yi. Saboda sun san gaskiya ake fada masa.
Amma kai da ya ke jahili ne ka zo kana zagi, to Ubanka ne Buharin? Ya bar iyayenka da yunwa..."

Jarumar fina-finan Kannywood Ummi Ibrahim Zeezee ta wallafa wannan batu ne a shafin ta yayin da wani masoyin Buhari ya yi mata raddi akan sukar gwamnatin sa da ta yi.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega