
Tun a farkon shekaran nan ake takun saka tsakanin Ali Nuhu da Adam A Zango, amma dalilin wannan Gaba shine har yanzu ba'a Gama sani ba. Sai dai akwai zargi daga dukkan bangarorin inda bangaren Zango suke cewa Ali Nuhu yana bakin ciki da cigaban da Adamun yake samu, yayin da su kuma banagaren Alin suke cewa na kusa da Adamun sune suke zuga shi domin ganin sun shiga tsakanin Adamun da Ali. Zargin da kowa ne bangare yasha musantawa. Abun ya fara fitowa fili ne bayan da Adam A zango ya saki fim dinsa mai suna Gwaska Return a Ado Bayero cinema inda wasu Jarumai maza da mata suka je amma ba'a ga keyar Ali Nuhun ba ko kuma na kusa dashi. Abun ya qara zafi ne bayan yaran Ali Nuhu sun yi ma Bello Muhammad Bello zagin qare dangi bisa zargin cewa yana habaici akan Ali Nuhu sannan yana zuga Adam Zango. BMB dai yayi rubutu ne kamar hakaYayin da yaran Ali Nuhun suka mayar masa da martani kamar haka
Tunda ake wannan maganganu ba wanda yace komai tsakanin Ali da Adamu, bayan faruwar dukkan wadan abubuwa Adamun ya fito yayi magana inda yace shifa rikicin sa ba da Ali Nuhu bane, inda daga bisani kuma yayi wani dogon rubutu kamar haka " B A U T A K O Z A L I N C I A Yau wasu daga cikin Jarumai MAZA da MATA tsofaffi da manya da kananan da wani bangare na Maaikata a kannywood. Suka kai kara da kukan wasu manyan producers da kananan su.! Gurin Hukumar tace fina-finai. Kan abin da suke kira danne hakki da mugunta da producers din suke musu. A cewarsu mafi yawan ayyukan da suke da producers din basa biyansu ko kuma in zaa biya ka a baka kudin da ko na mota bazai kai ba. Ko ayi kwanaki ana aiki da kai, in an gama ace za'a kiraka, shikenan an cinye. Tabbas duk abin da mutum sama da Ashirin Mata da maza suka fada, to lallai yana faruwa. Kuma hakan zalincine Allah bazai kyaleba.. Yaku masu wannan dabiar, ku sani an wuce lokacin bauta. Wadanda kuke bautarwa Allah sai ya saka musu. Kuma Wallhi sai kun biya su hakkin su a ranar da baku da komai sai abin da kuka jewa Allah dashi. Ina rokon wasu daga cikin Directors, Actors, Actresses, writers da producers. Mu hadu domin kawo karshen Wannan zalinci. Duk wanda aka samu a karbi hakkin wanda yaci kuma a hukuntashi. Muyi domin Allah bada nufin tozarci ko cin Zarafin juna ba. Sai Dan tsaftace Masana'anta daga hannun baragurbi. Ka fara daga set din da kake. Duk wanda kaji ba'a biya ba, ka dakatar da aikin har sai an biya hakkin mutane sannan a cigaba. Domin ni nasan ba'a film sai da kudi. The Wallhi duk KABON wanda kaci ka shirya sauraran hkunci tun daga kabari. Allah ka tsaremu da zalinci da cin dukiyar wadanda suka wahaltamana. Ameen. #gyaran_karaya_movement ". Inda daga nan kuma shima Ali Nuhu ya fito yayi kira ga masoyansa da kar su kara cewa komai, koda kuwa an zageshi suyi shiru dan shi baya zagi ko batancin ga abokin sana'arsa. Yanzu dai zamu iya cewa al'amurra sun qazance a kannywood wanda idan ba'a samu gyara da zaman lafiya ba za'a koma gidan jiya.







