Daga yanzu sai wanda ya iya Yarbanci zai shiga Makarantu da Jami’a a Legas
- Gwamna Ambode ya sa hannun kan dokar da za ta sa a rika amfani da yarbanci
- Babu wata Jiha cikin Jihohin Najeriya da ta taba kafa wannan doka kawo yanzu
Mun samu labari cewa daga yanzu koyar da yaren Yarbanci a Makarantun boko ya zama dole a Jihar Legas kuma sabawa wannan doka zai jawowa mutum tarar kudi. Kuma sai da yaren za a samu shiga Makarantun Jihar na gaba da sakandare.
An kawo wata doka a Ranar Alhamis da ta wuce da ta wajabta koyar da Yarbanci a Makarantun Bokon Firamare da Sakandaren Gwamnati da ma na ‘Yan kasuwa na Jihar Legas. Gwamna Akinwumi Ambode ya sa hannu a wannan doka.
Yanzu haka dai Gwamnatin Jihar Legas ta zama ta farko a Kasar da ta wajabtawa jama’a koyon yaren gida. Kwamsishinan shari’a da sauran Kwamishionin Jihar su nan a lokacin da Gwamnan na Legas Ambode ya rattaba hannu kan dokar.
Bayan nan dai Gwamnatin Jihar Legas ta kawo wasu sababbin dokoki har 6 da za su shafi fannin kiwon lafiya da wutan lantarki a Jihar. Sabawa wannan dokar ta aiki da yaren yarbanci a fadin Jihar na iya jawowa mutum tarar N500,000.