
Wani direba mai shekaru 42 a duniya yana gwagwarmaya kan rayuwarsa a wani asibitin kudi dake Asaba, jihar Delta, bayan ya samu sabani da wata karuwa.
Bisa ga rahotanni, karuwa ta ciji wani mutun azzakarinsa, sakamakon kin biyanta kudinta bayan ta gama biya masa bukatar san a tsawon dare daya. Direban wanda aka fi sani da Ogaga, yana aiki a kamfanin tuki dake kai kawo tsakanin hanyar Onitsha-Asaba-Lagas a kullun.
A wannan ranar, Ogaga ya kai pasinjojinsa daga Jihar Lagas zuwa Asaba, maimakon ya kwana a gurin da kampanin ta tanada domin direbobi, sai ya yanke shawarar kwana da karuwa a hanyar Okpanam. Sun yarda a kan zai biyata naira 15,000 idan ta kwana da shi, amma bayan matar ta biya masa bukatunsa a daren, Ogaga yaki biyanta cikakken kudi, kan cewa karuwar bata biya masa bukatunsa ba yanda yayi tsamani.
Ya kuma ce ya siya mata abin sha da farfesu a daren kafin su kwana
Duk da haka karuwar ta nace kan cewa lallai sai ya biyata cikakken kudinta, wannan ne ya sa fada ya kaure tsakaninsu. An ce mutumin yayi mata duka. A kokarinta na ceton kanta, ta rike azzakarisa ta kuma gantsara masa cizo a kan azzakarin, wanda saura kadan kan kaciyarsa ya cire.
Ihun da yayi ne ya jawo hankalin mutanen dake cikin hotel din. An kais hi asibiti cikin gaggawa inda yake ganin likita a yanzu.



