
Goodluck Jonathan ya taya yan Najeriya murnar shiga sabuwar shekara
- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya shawarci yan Najeriya da su daina dangana kalaman batanci ga kasar
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana abubuwan da ‘yan Najeriya ya kamata su yi da zai sa shekara 2018 ya fi shekara 2017 albarka.
Jonathan ya bayyana haka ne sakon sa na shiga sabuwar shekara, inda ya shawarci 'yan Najeriya su rika furta kalaman alheri akan kasar da kuma kaunar juna.
“Duka mu muna kaunar Najeriya kuma muna mata fatan alheri, duk da irin matsalolin da ta ke fuskanta ba dai-dai bane mu rika furta munanan kalamai akan Najeriya. “Ya kamata mu rika fadan kalaman alheri akan Najeriya. Idan muka yi haka, shekara 2018 za tafi shekara 2017 albarka musamman idan muka yawaita yi mata adu'a masu kyau a duk lokacin da muka tashi daga barci da safe. “Ina rokon Allah ya biya wa duka yan Najeriya bukatun su na alheri a cikin wannan sabuwar shekara da muka shiga. "Ina muku barka da shiga sabuwar shekara sako daga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan (GEJ).



