Shahararren jarumin nan mai wasan barkwanci a dandalin shirya fina-finan Kannywood, Muhammadu Sani Ibrahim Tsiga wanda aka fi sani da Dangwari ya bayyana dalilan da su ka sa ya rungumin bangaren barkwanci. A cewar jarumin, marigayi Rabilu Musa (Dan Ibro) shine ya sa masa sha’awar shiga wasan fina-finan Hausa.
Jarumin ya kasance dan asalin jihar Katsina kuma haifafan jihar Kaduna.
A cewarsa marigayi Dan Ibro ne ya karfafa masa gwiwar kwaikwayon gwari domin a cewar sa babu mai wannan baiwar ta kwaikwayon gwarawa a fim. Wato kenan kwaikwayon gwarawa ya zame masa jari.
Dangwari ya bayyana cewa ya so ya bar harkar fim a lokacin da labarin rasuwar Dan Ibro ya riske shi amma sai ya ga haka Allah ya tsara don haka ya ci gaba da sana’ar ta sa.,



