Home

Music

Video

Kanny

Zuwan Adam A Zango taron Maulidi yabar baya da kura



Adam A Zango ya halarci taron maulidi da akayi a Gidan Alan waka a garin kano, bayan tashi daga taron Adamun ya saka wadansu dauka da akayi a wajen maulidin Inda aka samu wasu suna Nuna jindadinsu naganin Jarumin a wajen taron maulidi, yayin da wasu kuma suke Jin hakan bai kamata ba saboda a wajensu suna ganin ba kyau maulidi. Jarumin ya mayar musu da martani acikin wani hoton bidiyo da ya tura a shafinsa na sada zumunta inda yake cewa " Shi Ilimi kogi ne inda ka sani ka tsaya inda baka sani ba kar ka nemi wucewa inda baka sani ba. ya kara da cewa " yawancin mutanen da suke wannan maganar cewa ba kyau maulidi suna so ayi musu Happy Birthday sai manzon Allah ne bakwa so ayi masa ? Gara in manta Birthday dina akan na in manta Bithday din manzon Allah". Bayan wani lokaci kuma Adamun ya cigaba inda yayi wani rubutu kamar haka: "Duk irin laifin da musulmi yake aikatawa....idan ya kasance mai yawan istigfari.....mai yin ibada....mai son Manzon ALLAH S.A.W....mai gudun aikata shirka..... Toh baikamata Dan Adam ya ya yanke masa hukunci ba.....tunda babu Wanda baya aikata laifi a duniya in banda ANNABI MUHAMMADU S.A.W...... Don haka la'antar Dan uwanka musulmi ba naka bane Dan uwa.....tunda babu wani Wanda yafi a wurin ALLAH S.W.T sai wanda yafi tsoronsa......Shi kuma tsoron ALLAH a zuciya take ba'a.... Suffa ko sutura ko kamanni ko nasaba ko dukiya ko daukaka ko kwalliya ko kyauta ko iya magana ko iya kira'a ko fadan a ALLAH a baki Bane .....Don ALLAH mu kiyaye yan uwana... KAI DAI KAGA MUTUM."

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega