Home

Music

Video

Kanny

“Yadda Na Zama Zainab Komai Da Ruwanki”


A duk Mako, wannan Filin yakan kawo maku takaitaccen tarihi ne na yadda wasu daga cikin ’Yan uwanku Mata suka yi fice, a wasu wuraren ma suka yi zarra a kan wasu imma, Sana’o’i, ko kuma harkar karatun Addini ko na zamani. Duk wannan dai manufa dai ita ce, mu dauki abin da za mu iya koyi da shi, ko mu ma rayuwarmu da ta iyalanmu za ta haskaka kamar yadda tasu ta haskaka. A wannan satin muna tafe maku ne da takaitaccen tarihi da kuma bayanan harkokin da Malama Zainab Ahmed Usman Chanchangi, wacce wasu ke mata la’akabi da komai da ruwanki, ta sanya a gaba, wadanda kuma suke ta Haifa mata, ‘Ya’ya masu ido, ba kuma ita kadai ba, iyalanta, da al’umma duk suna cin gajiyar wannan hobbasan nata. Da fatan za mu dauki darussan da ke cikin wannan gajeruwar tattaunawar, a sha karatu lafiya: Za mu so jin cikakken Sunanki da kuma takaitaccen Tarihinki? Suna na, Zainab Ahmed Usman Chanchangi. An haife ni a Kaduna, na fara Makaranta a “Unikue International School.” Daga nan na koma Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da ke Tudun Wada, inda na kammala karatuna na Firamare. Na tafi ‘FGGC Bakori, inda na fara karatuna na Sakandare, har sai da na kai SS1. Daga nan, na dawo, ‘Danbo International School.’ Na kuma yi Makarantar Kimiyya Da Fasaha ta Kaduna, inda na yi karatun Digiri dI nan a farko da na Biyu. Na kuma halarci cibiyar NTI, wajen da na samu shaidar PGDE. Hari la yau, na sami shiga Jami’ar Jihar Kaduna, ‘KASU,’ nan kuma na sami shaidar, ‘PGENT.’ A yanzun kuma zan fara karatuna na Masters ne, watau Digirin-Digirgir, nan ba da jimawa ba. Ina da Aure, da ‘Ya’ya, Alhamdulillah. Wane irin aiki kike yi a yanzun? Ina aiki ne a Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, wacce a Turance ake kira da, Kaduna Polytechnic, a sashen da ake kira, ‘Department of Cooperatibe Economics & Management, wanda a Hausance a kan kira shi da, Sashen Nazarin Tattalin Arziki na Gamayya da Gudanarwa. Ta ya ya kike iya hada dawainiyar aikinki, da kuma hidindimun iyalinki? Alhamdulillah, ina mutukar jin dadin aikina, saboda ina samun isasshen lokacin duba ‘Ya’yana da Mijina. Saboda shi aiki na koyarwa shine aiki da mace za ta yi cikin kwanciyar hankali. Domin aiki ne na wasu awowi, har ma kina iya hadawa da wata sana’a taki in kin so. Domin kamar ni, baya ga wannan duka, ina kuma hadawa da sana’ata, nakan sayar da kayayyakin misali Tufafi, na Yara, Mata, Maza da Mata. Kai duk hanyar halas da ta bullo mani matukar na duba nag a zan sami karuwa a cikinta ni da iyalaina, to nakan jarraba ta. Musamman kasantuwa ta Mace, to ni ban yarda da zaman banza ba. Sannan ma, ni da wata aminiyata, muna gudanar da harhar shirya bukukuwa, wanda a Turance akan kira da, ‘Ebent Planning.’ A takaice dai, ga ki Malama a Jami’a, sannan kuma ga ki ‘Yar Kasuwa kenan ko? Eh, Allahamdulillah, lallai hakane kamar yadda na fada miki, ke karewa ma, hatta kayan Aure a kan bani kwangilar hada su, sannan kuma a kan gayyace ni domin na zo na adamta gidan Amarya, na kawata shi sosai. To ko za ki yi mana karin bayani dangane da shi wannan, ‘Ebent Planning’ din da ki ka ce kuna yi? Tabbas kuwa, da zaran kun same ni, abu na farko dai shi ne, na nemi bayani daga gare ku, kan wane irin buki ne ku ke so ku yi? Sannan kuma, ya yanayin qarfinku yake? Saboda shi sha’anin adamta waje, ya danganta ne da yanayin qarfin aljihunka, watau, ‘Iya Kuxinka, iya shagalinka.’ Na gargajiya ne ku ke son shiryawa, ko na zamani ne, duk dai muna shiryawa. A nan Kaduna ne kawai za a iya gayyatarku, ko har wani garin daban ma za a iya gayyatarku domin shirya bikin, ko gyaran xakin Amaryan? In sha Allah, duk inda aka gayyace mu a shirye muke da mu je, ai shi mai nema, ba shi da nesa, matuqar dai zai samo. To mu dawo batun abinci da kuma kwalliya, da ki k ace kuna yi, shima namu na nan ne kawai, ko har da na waje. Ai duk ya danganta ne da abin da mutum yake so, kuma yake da qarfin xauka. Mukan shirya abincin gargajiya kala-kala, kamar yadda mukan yi na zamani kalan na qasashe daban-daban. Da kwalliya da abincin nan, mukan yi namu na gida nan, mun kuma iya haxa na Larabawa, Indiyawa, Turawa da dai sauransu. To shin duk waxannan nau’ukan Kwalliya da Abincin, a waje ne ki ka je ki ka koyo su, ko ya abin yake ne? A gaskiya ni ban je waje koyo waxannan ayyukan ba. Amma dai ni tun ina Yarinya qarama, ni mai son girke-girke ne. na kuma yi karance-karance da dama a kan hakan. Sannan kuma sai Allah Ya haxa ni da wata kamata, wacce take ita kuma qwararriya ce a duk waxannan fannonin. Wannan haxin gwiwa namu ya sanya ba mu tava samun wata matsala ba, a duk abubuwan da muke yi. To kasantuwar ki Mace, kuma Malama mai karantarwa a Jami’a, ko kin tava gamuwa da wata matsala,musamman daga vangaren Xalibanki? A’a, a gaskiya ni ban tava fuskantar wannan matsalar ba, saboda ni xalibai na, abokai na ne, na xauke su, a matsayin qanne na, kuma tamkar ‘Ya’yana ne na xauke su. Suna kuma matuqar darajanta ni, suna bani girmamawar da ya kamata. Malama Zainab, a sama kin xan yi nuni a kan ayyukan taimakon al’umma, kamar na NGO, shin ko kina kuma da wani shiri ne a kan hakan? A gaskiya kamar yadda na shaida maki, ni Uwa ce, sai kuma Allah Ya bani wata kyauta inda Ya jarraba ni da yaro wanda bai cika lafiya. Wanda akasari ana samun irinsu ne kimanin yara 10 cikin 100, Wanda Turawa ke ce masu ‘Autism, Downstream, Spectrum, Down Syndrome, da dai sauransu. Mu kuma a Hausa za ki iya ganin wani yaron wawa-wawa ne, wani yana da farfaxiya, wani a ce Aljannu, ga su nan dai iri-iri, abin tausayi cikin Al’umma. Da yawa iyaye ba su san waxannan lalurorin kusan duk akwai maganinsu a asibiti ba, sai a vige da kai yaro gidan ‘Yan tsibbu da ‘Yan bori. Ko kuma a qyale Yaro ya yi ta garari a titi, ina kukan zuci duk sanda na haxu da masu iren waxannan lalurorin. Wani za ki ga miyau yake zubdawa, wani ba ya tafiya, wani ba Magana, ga su nan dai da yawa. A shekarar da ta gataba, na yi wani shiri a gidan Talabijin ‘DITV,’ wanda mun tattauna da Aliyu Tahir, bisa wannan matsalolin da suka addabi al’umma, sannan kuma gwamnati ba ta agazawa. Su waxanan yara akwai bukatar taimako da suke bukata. Wanda matuqar kana da halin taimakawa ya kamata ka taimaka. Misali ko irin gwaje-gwajen su asibiti kuxi ne mai tsada, maganin da su ke sha ma hakan. Hakanan idan makaranta za a kai su, makaranta ba irin ta yaran da bas u da wannan matsalar ba ce. Ina ma ganin kalar makarantansu da ke garin nan, ina jin ba su fi Biyu zuwa Uku ba. Wanda xan talaka bai isa zuwa ba. Ko kuna da hali akwai gajiya saboda su makaranta kuxi suka sani, ba su san ba bu ba. A wanan lokacin da na yi shirin, wallahi na samu qorafi sama da dubu, masu irin wanan lalurorin. Don na taimaka na yi qoqarin nema, amma ba mu samu waxanda za su taimaka mana da kuxi ba. Sai na samu guri da za a gyara a nemi wanda za su koyar da yaran nan yanda za su tafiyar da rayuwarsu, saboda akasarinsu ba su iya yi wa kansu komai, amma ban samu taimako yanda ya kamata ba. Babban burina a rayuwa, Allah ya hore min in inganta rayuwa irin ta waxanan yaran. Ko kina da wani saqo da za ki aikawa mutane To saqona zuwa ga masu hali ne da kuma gwamnati, idan Allah Ya hore maka, to ka zo mu haxa hannu mu taimaki yaran nan, masu bukatar taimako. Aikin lada ne na duniya da lahira, ya fi kyautar neman suna. Sannan iyaye masu ire-iren waxannan yaran, ku yi haquri mu rungumi yaranmu, kyauta ce Allah Ya ba mu, sai mu gode ma shi. Allah Ya ba da sa’a, mun gode sosai da lokacinki da ki ka ba mu. Ba komai, Allah Ya saka da alheri, Ya xaukaka ki a bisa aikinki da mu baki xaya.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega