Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da cewa a halin yanzu dan Shugaban Kasa, Yusuf Muhammad Buhari ya kwance a wani asibiti da ke Abuja bayan ya yi hadari da Babur a daren jiya a yankin Gwarimpa da ke Abuja.
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya bayyana cewa Yusuf ya samu kariya a hannu da kuma rauni a kansa amma ya nuna cewa yana ci gaba da samun sauki. Ya kara da cewa Shugaba Buhari da Uwargidansa na barar addu'a ga dan nasu don ya samu lafiya.



