Home

Music

Video

Kanny

Harin da aka kai wani Masallacin garin Mubi da safiyar nan ya rutsa da rayuka da dama


Wani matashi dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wani masallaci dake garin Mubi, jihar Adamawa a safiyar yau - Al’amarin ya afku ne da misalign karfe 5:20 na asuba, bayan sallar asuba; an rahoto cewa mutane 30 sun rasa rayukansu - Kakakin yan sandan jihar Adamawa ya tabbatar da al’amarin inda ya bayyana cewa wadanda suka ji rauni na asibitoci daban-daban inda suke karban kulawa Wani tashin bam ya afku a wani Masallaci dake garin Mubi, jihar Adamawa, a safiyar yau, Litinin, 21 ga watan Nuwamba, jaridar Punch ta ruwaito. An rahoto cewa al’amarin ya afku ne a Kunu Araha, wani yanki na Arewacin Mubi, da misalin karfe 5:20 na safe.

Majiyarmu ta tattaro cewa akalla sama da mutane 30 ne suka rasa rayukansu a bam din da matashi dan kunar bakin wake ya tayar.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega