Home

Music

Video

Kanny

An Kama Wani Da Ya Yi Garkuwa Da Yaron Yayansa A Kano



An Kama Wani Da Ya Yi Garkuwa Da Yaron Yayansa A Kano Rundunar 'yan sanda jihar Kano ta cafke wani mai suna Samuel dan asalin Jihar Benue mazaunin unguwar Birgade dake karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano, inda ya yi garkuwa da dan yayan sa mai shekara tara, ta hanyar sace shi akan hanyar sa ta komawa gida daga makaranta.
Samuel ya nemi mahaifin yaron da ya bada naira miliyan biyu kafin ya sako shi. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano DSP Majia, ya bayyana cewa rundunar su ta samu nasar ceto yaron ba tare da biyan ko sisi ba, sannan wanda aka kama din yana tsare a hannun su domin fadada bincike kafin daga bisani su maka shi gaban kotu.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega