Home

Music

Video

Kanny

Raba kasa: Arewa ta fitar da matsayar ta bayan wani muhimmin taro


Shugabannin Yankin na Arewa sun yi wani taro game da tsarin Najeriya - Dattawan Yankin sun ce sam ba su gudun a koma tsarin da kasar ta ke da - A halin yanzu dai ko ina ya dauki kukan yi wa tsarin Najeriya garambawul Kwanan nan Shugabannin Yankin Arewa su kayi wani taro game da matsayar su game da tsarin Najeriya a dakin taro da ke Arewa House a Jihar Kaduna.
Tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello watau Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana irin kokarin da Arewa tayi shekarun baya lokacin an samu ‘yancin kai yace ba su ki ba a koma tsarin da ake a shekarar 1914 ko kuma tsarin 1960 lokacin da ake da bangarori 3 na Arewa da Yamma da Kudu.
Dr. Usman Bugaje wanda shi ne jagoran zaman taron ya bayyanawa ‘Yan jaridar Daily Trust cewa tun can Arewa ba ta goyi bayan wannan tsari ba a lokacin da Shugaba Janar Aguiyi-Ironsi ya sauyawa kasar fasali. Shi ma dai Bugaje ya nuna cewa Arewa ba ta gudun ayi garambawul. Gwamnan Jihar Sokoto kuma Shugaban taron Aminu Tambuwal yace ko kadan ba wai Arewa tana karuwa da tsarin da ake tafiya bane don haka ta hakinkace a bar Kasar a haka. Manyan dai sun ce za su kara tuntubar Jama’a kafin a dauki mataki na gama-gari.
Naijhausa

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega