Home

Music

Video

Kanny

Dalilin da zai sa ku kalli wadannan sababbin fina-finan hausa guda 5


Duk farkon shekara ake sakin sababbin fina-finai domin nishadantar tare da fadakar da masu kallo. Amma a wasu lokutan masu shirya fina-finai kan sake sakin wasu fina-finan a tsakiya ko kuma karshen shekara. Ga wasu jerin fina-finai guda 5 da marubuta da furdososhi da jarumai suka taka rawar burgewa cikin shirin.
1. Rariya: Fitacciyar 'yar wasa Rahama Sadau ta dauki nauyin shirin.
2. Kalan Dangi: Shirin babban darekta Ali Gumzak, kuma shahararriyar 'yar wasa Aisha Aliyu Tsamiya ta dauki nauyin shirin.
3. Mansoor: Ali Nuhu ne ya bayar da umarnin shirin, sannan Umar M. Shariff da sabuwar 'yar wasa Maryam Yahaya suka fito a jarumai.
4. Rumana: Shirin kamfanin Hikima multimedia mai dauke da fiattun jarumai kamar su; Rahama Sadau, Adam Zango, da Aminu Shariff Momo.
5. Kujerar Wuta: Shirin na dauke da gogaggiyar tsohuwar tauraruwa, Hauwa Maina, wacce ake wa kirari da "mai idon zinare".

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega