Home

Music

Video

Kanny

Dalilin Da Ya Sa Buhari Ya Nemi Bankin Duniya Ya Mayar Da Hankali A Arewa- Fadar Shugaban Kasa



A yayin da ake ci gaba da ce ce ku ce sakamakon ikirarin da Shugaban Bankin Duniya ya yi kan cewa Shugaba Buhari ya umarci Bankin ya mayar da hankali wajen bunkasa Arewa, Fadar Shugaban kasa ta yi karin haske kan cewa tun lokacin da aka rantsar da shi, Shugaba Buhari ke neman kasashen duniya su taimaka wajen sake gina yankin Arewa maso Gabas wanda rikicin Boko Haram ya kassara. Kakakin Shugaban, Femi Adesina ya ce wasu mutane sun ba kalaman Shugaban Bankin wata ma'ana kamar cewa ya fifita Arewa a kan sauran yankunan kasar nan inda ya nuna cewa Buhari ya fi damuwa ne da wadannan jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa wanda a kan haka ma ya nemi kasashen su zo su gina yankin a maimakon su turo kudade.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega