Home

Music

Video

Kanny

Yan bindiga sun harbe mutane 4 a harin yankin kabilar Hausawa na jihar Delta


Mutane hudu sun rasa rayukan su a wani hari da 'yan bindiga suka kai wani yankin kabilar Hausawa na garin Asaba dake jihar Delta. Harin da 'yan bindiga suka kai wani yankin hausawa da fulani da misalin karfe 10:00 na dare a ranar Jumma'ar da ta gabata, yayi sanadiyar raunata da dama da kuma rasa rayukan mazaje uku da mace daya. Yan bindigar sun budewa al'ummar wuta dake yankin kasuwar Abraka na unguwar Cable point, baya ga haka kuma suka jefa bam cikin wani masallaci.

Jaridar VANGUARD ta ruwaito cewa, wani bahaushe ya yi ta maza yayin da ya dauki bam din da hannunsa kuma ya jefa shi cikin wani kogi tun kafin ya fashe. Rahotanni daga shafin DAILY POST sun bayyana cewa, dakarun soji da jami'an 'yan sanda ne suka garzaya da wadanda suka samu rauni zuwa asibiti bayan sun kwantar da tarzomar.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega