Farfesa Andrew Nok, kwamishinan ilimi a jihar, wanda ya wakilci gwamna Mal. Nasiru el-Rufa'i a taron budewa, ya ce, "Wannan ya isa yabo ga NAF da shugaban ta, Cif Air Mashal Sadique Abubakar, saboda wannan aikin duk al'ummar Kaduna aka yi wa; kuma yara zasu amfana da ita sosai."
Shi kuma Cif Air Mashal din ya ce wannan na daya daga cikin aiyukan da NAF ta fara saboda gyara harkar tsaro a kasa, da kuma taimakawa ga karatun 'ya'ya mata.
Daga cikin gyararrakin da aka yi wa tsohuwar makarantar, ya hada da gine-ginen sababbin bangarori, sa alluna na zamani da komfiyutoci a ajujuwa.
A da makarantar na daukar daliban jeka-ka-dawo 540, amma saboda gyaran da aka yi, yanzu makarantar zata iya diban daliban kwana har 720. In aka duba a aiyukan NAF na 'yan shekarun nan da suka wuce za'a ga ta gyara makarantun sakandare a garuruwan Uyo, Ibandan, Enugu, Shasha (a jihar Legas), da kuma a Jos. Wannan na daga cikin mujaddadin NAF na taimakawa ci gaban kasa a karni na 21.
Bayan wannan kuma, NAF ta dauki nauyin diban malamai da kuma horar da su don su kware su zama malaman makarantun.NAF ta ce samun kyakkyawan ilimin al'umma na daga cikin manyan abubuwan da suke kara tsaron kasa.
Wadanda suka halarci taron budewar sun zaga makarantar sun ga sababbin gine-ginen da aka yi, wanda sun hada da dakin malamai, filin asembili, dakuna, laburare, dakin bincike, dakunan karatu, da dakin komfiyutoci, da dai sauran su.



