Shafin mu ya bankado daga kididdiga ta binciken jama'a akan wadanda suka kere kowa kudi a nan Najeriya, wanda kuma ko shakka ba bu Alhaji Aliko Dangote ya kere kowa.
A wata ruwaya daga maganganun al'umma sun bayyana cewa, ana yiwa Dangote mai kudin bakar fata a duk duniya domin a cewar su indai mutum baki ne to kuwa Dangote ya fi shi kudi.
Ga jerin sunayen mutane 10 na Najeriya da suka yi fice wajen tarin dukin da masana'antunsu ko kuma sana'ar su:
1. Alhaji Aliko Dangote - Mai gidauniyar Dangote
2. Mike Adenuga - Mai kamfanin Con oil da kamfanin sadarwa na Globacom
3. Femi Otedola - Mai kamfanin Forte oil
4. Orji Uzor Kalu - Mai gidauniyar Slok
5. Cosmos Maduka - Mai gidauniyar Coscharis
6. Jimoh Ibrahim - Mai kamfanin inshora na Nicon da kuma Global Fleet
7. Jim Ovia - Bankin Zenith da kamfanin sadarwa na Visafone
8. Pascal Dozie - Kamfanin sadarwa na MTN da bankin Diamond
9. Oba Otudeko - Gidauniyar Honeywell, kamfanin mai na Pivotal da kamfanin sadarwa na Airtel
10. Alhaji Sayyu Dantata - Gidauniyar mai na MRS
Source: Naijhausa



