Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Laraba. Tuni dai gwamnati ta kwace wasu daga cikin kaddarorin ta. ''Ina son ku sani cewa babu wanda zai tsallake hukunci. Muna ma shirin taso keyar Diezani ne alhali bincike yana gudana''. In ji shi.
Ya kara da cewa ''mun kawo matakin da babu wanda ya isa ya hana mu yakin cin hanci da rashawa amma dole mu fahimci cewa wannan yaki ya shafe mu ne gaba dayan mu don cigaban al'umma mai tasowa''. Magu ya ce cin hanci da rashawa ne silan gwagwarmayar neman raba kasa da yajin aiki da sauran tsiyatakun da suka wa kasar kanta. Ya ce hakkin mu ne mu gyara duk wani abu da cin hanci da rashawa ya lalata.
Magu ya ce tarbiyya daga gida take fatawa. Don haka ya yi kira da a fito fili a sanar da su game da duk wani jami'in hukumar ta su ta EFCC da ya jefa kan shi cikin lamarin cin hanci da sharawa. Source: Naijhausa



