Home

Music

Video

Kanny

Kalli Abinda Dan Boko haram yayi ma wani karamin yaro a garin chibok(Hotuna)


Wasu hotunan ban tausayi sun bayyana na wani yaro wanda wani dan Boko Haram yabi ta kansa da babur a daren da yan Boko Haram din suka sace yan matan Chibok. Wannan yaro da jafa’in nan ya afka masa sunansa Ali Ahmadu, kuma shekarunsa 6, a daren da yan Boko Haram suka saci matan Chibok ne daya daga cikin yan ta’addan ya bi ta bayan Ali Ahmadu akan Babur, wanda hakan yayi sanadiyyar balla masa kashin baya. Majiyarmu ta ruwaito wani ma’abocin shafukan Facebook George Onmonya Daniel ya bayyana wannan labari a shafinsa, inda yace a jiya ne wani bawan Allah Nuhu Fulani Kwajafa ya kawo shi garin Abuja, don garzayawa dashi kasar waje inda ake sa ran bashi kulawa na musamman. Tun bayan da wannan lamari ya wakana, Ali bai sake taka kafarsa ko motsawa ba, har sai yanzu da wata kungiya mai zaman kanta ta taimaka masa da yunkurin kais hi kasar wajen domin samun kulawa.

Ana bukatar jama’a da’a taimaka ma Ali Ahmadu ta hanyar aikawa da kudi zuwa asusun kudi na bankin Eco, mai suna Global initiative for peace, love and care. Da lambar asusu: 3362017526. Ko a samu Nuhu Kwajafa akan lambar waya: 0816 318 3797.

Soure : Naijhausa

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega