Goodluck Jonathan ya kalubalanci jamÃyyar APC akan ikirari da tayi - Ya nemi tayi bayani a kan naira triliyan 14 da sauransu - Jonathan ya nemi ba'asin dalilin da yasa Najeriya zata je rance duk da kudin da gwamnati tace ta kwato Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi tir da ikirarin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na cewa ya sace dukiyar jama’a a lokacin gwamnatin sa. Tsohon shugaban kasar ya bukaci gwamnatin APC da tayi bayani dalla-dalla kan naira triliyan 14 wanda yayi ikirarin cewa ya yi kasafin su cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ya kuma bukaci jam’iyyar mai mulki da tayi bayani ga yan Najeriya kan dalilin da yasa duk da ikirarin tan a kwato kusan naira triliyan 2 daga gwamnatinsa a matsayin kudin sata, amma duk da haka Najeriya ke son aro naira triliyan 1.6.
Yana maida maratani ne kan wata sanarwa daga sakataren labarai na jam’iyyar APC ta kasa, Bolaji Abdullahi, inda yace “Babu wanda yayi sata irin Jonathan”.
Jonathan ya bayyana a shafinsa na Facebook, cewa abun dariya ne ace babu wani hujja na sata da aka gabatar a kan shi, amma duk da aka kakakin APC, Abdullahi Bolaji yace ya saci dukiyar kasa. A wata sanarwa da Reno Omokri ya wallafa a madadin sa, ya bayyana cewa duk da cewar “hujjoji da dama” sun nuna cewa tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha ya saci kudi, gwamnatin APC ta amince da cewar bai yi sata ba.



