Bashir Ahmad ya bayyana halin lafiyar Shugaba Buhari - Mai taimakawa Shugaban kasar yace ya murmure yanzu - Ta kai yace Gwamnatin Buhari ta na yi da 'Yan kasuwa Daya daga cikin masu taimakawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana halin lafiyar sa inda yace yanzu Shugaban ya murmure. Bashir yace Shugaban kasar ya samu lafiya inda yake maida martani ga masu kishin-kishin din cewa har yanzu bai samu lafiya ba ganin yadda ya gagara gabatar da jawabi wajen bikin kaddamar da Kamfanin Olam a Garin Kaduna inda sai dai Ministan harkar noma na kasar Audu Ogbeh ne yayi jawabi. Mai taimakawa Shugaban kasar yace tun da har Shugaban ya samu zuwa Jihar Kaduna babu maganar ace har yanzu bai samu lafiya ba. A maganar jawabin sa kuma ya bayyana cewa Kamfanin Olam na 'Yan kasuwa ne ba na Gwamnati ba kuma Shugaban ya je ne domin nunawa masu baza hannun jari cewa Gwamnatin sa na yi da su. Bashir Ahmad wanda ke taimakawa Shugaban kasar a kafafen zamani ya bayyana wannan ne wata hira da yayi da Majiyarmu kwanan nan a Garin Abuja.
Hadimin Buhari Ya Bayana Halin Da Shugaban Kasa Yake Ciki Na Rashin Lafiya

Share this
|
|