Home

Music

Video

Kanny

EFCC ta sake gano wani katafaren ginin Naira biliyan 6 na Patience Jonathan a Abuja


Hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar Najeriya tu'annati zagon kasa watau EFCC a taikaice ta sanar da cewa ta gano wani katafaren gini mai hawa 8 mallakar uwar gidan tsohon shugaban kasar Najeriya Patience Jonathan a Abuja. Shi dai wannan katafaren ginin da ba'a kaiga gamawa ba kamar yadda hukumar ta bayyana har yanzu ba'a kayyade ainihin kudin sa ba a kasuwa sai dai wasu dillalai sun bayyana cewa zai yi darajar Naira biliyan 6 a kasuwa.

NAIJ.com dai ta samu cewa wakilin majiyar mu da ya ziyarci katafaren ginin ya ce yana a kusa ne da unguwar nan ne ta Central Business District a turance a tsakanin masallacin Abuja da kuma babbar ma-akatar gwamnatin tarayya. Binciken farko-farko da hukumar ta EFCC tayi dai ya tabbatar da sa hannun wasu manyan makusantan uwar gidan mataimakin shugaban kasar Patience Jonathan a saman takardun gidan.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega