Majiyarmu haka ma dai ta samu cewa fadar shugaban kasar Najeriya ta yi kaca-kaca da wata tsohuwar ministar tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo kuma shugabar kungiyar nan dake fafutukar ganin an sako yan matan Chibok daga kungiyar Boko Haram mai suna Uwargida Oby Ezekwesili. Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai taimakawa shugaba Buhari ta hanyar yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar inda ya shawarci tsohuwar Ministar da ta sa kunya a ranta ko da sau daya ne ta yi tofin Allah-tsine ga yan uwanta masu fafutukar ganin sun kafa kasar Biyafara. Naijhausa



