Home

Music

Video

Kanny

Dandalin Kannywood: Har yanzu ban fidda ran dawowa harkar fim ba - Zainab Indomie


Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood wadda aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa tana sa ran zata dawo harkar fim gadan-gadan ta kuma yi fice nan ba da dadewa ba. Shaharraiyar jarumar wadda a yanzu haka tauraruwar ta ta riga ta dishe ta bayyana cewa tana nan tana murmurewa tana kuma kara kammala shire-shiren ta domin ta dawo da karfin ta ta kuma disashe taurarin wasu jaruman a harkar yanzu. Majiyarmu dai ta samu cewa a kwanakin baya anyi ta rade-raden cewa jarumar tana fama da wata matsanaciyar rashin lafiya ne da kuma ta ke hana ta walwala da harkokin nata kamar yadda ta saba.

Haka ma dai a baya jarumar ta fito a kafafen sadarwar zamani inda tayi tofin Allah-tsine ta kuma sha alwashin yi wa duk wanda ya kara cewa tana fama da kanjamau Allah ya isa.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega