A kokarinsa na wanke kansa daga zargin satar kudi, da cin hanci da rashawa, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, inda yace bai taba satar ko kwabon gwamnati a yayin dayake gwamnati. Atiku ya bayyana haka ne a ranar Litinin 11 ga watan Satumba yayin daya kai ziyarar duba sabon kamfanin buga takardu na Yaliam a unguwar Jabi, dake babban birnin tarayya Abuja.
Atiku yace duk abinda ya tara, ya same su ne sakamakon zafin nema irin nasa, inda yace yan Najeriya suna yi masa kallon barawo ne, saboda basu yarda mutum zai iya arziki hakanan ba, ba tare da yayi sata ba.
Yan Najeriya suna ganin babu yadda mutum zai yi kudi ba tare da yayi sata ba, abin na damu na, ta yadda ake yayata zargin rashawa a kai na, bayan mutanen dake wannan zargin sun kasa kawo hujja kwakkwara akaina. “Mutanen da suke zargina da sata, suna yi ne domin a tunaninsu kowa barawo ne kamar su, idan kuma sun ce Atiku barawo ne saboda nasarorin daya samu a rayuwa, toh yan adawa na su fada min inda suka samu kudi.” Inji Atiku. Daga karshe Atiku ya kalubalanci duk masu zarginsa da sata a zamanin dayake hukumar Kwastam da lokacin dayake mataimakin shugaban kasa da suka kawo hujjansu, ko su kai shi kotu. Dayake karin bayani akan batun wani Sanatan Amurka, William Jefferson, wanda ake zargi da alakar cin hanci da rashawa tsakaninsa da Atiku, Atiku yace har aka kammala shari’ar Jefferson a shekarar 2009, ba’a taba ambaton sunansa ba, ko aka kama shi da laifi ba.
Ku biyomu A shafinmu na facebook




