Home

Music

Video

Kanny

Gwamna Yari ya bayyana abunda Buhari ya fada masa game da Osinbajo


Gwamna Yari ya bayyana abunda Buhari ya fada masa game da Osinbajo Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Alhaji Abdulaziz Yari ya bayyana abunda Buhari ya fada masa a birnin Landan - Ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fada masa cewa ya sanar da gwamnonin Najeriya da su yi imani a shugabancin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo - Buhari wanda ya kwashe tsawon kwanaki 100 a birnin Landan don jinya, ya mika mulki ga Osinbajo kafin ya tafi hutu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fada ma gwamnonin jihohi 36 na kasar da suyi imani da shugabancin mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo. New Telegraph ta rahoto cewa shugaban kungiyar kwamnonin Najeriya, Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar ya fada ma abokan aikinsa a ranar Talata 5 ga watan Agusta cewa wannan shine sakon da shugaban kasa Buhari ya aiko ga gwamnoni lokacin da ya jagoranci sauran gwamnoni shidda zuwa ziyartan sa a Landan a watan da ya gabata. Hausa ta tattaro cewa Yari wanda ya kasance gwamnan jihar Zamfara, ya jagoranci gwamnonin Akwa Ibom, Oyo, Kano, Benue, Borno da na jihar Ebonyi a wani ziyarar fatan samun lafiya da suka kai ma Buhari Landan a ranar 26 ga watan Yuli. Ya kara da cewa Buhari ya gode masu bisa yadda suka riki Najeriya gaba daya a bayan idonsa. Buhari wanda ya kwashe tsawon kwanaki 100 a birnin Landan don jinya, ya mika mulki ga Osinbajo kafin ya tafi hutu. Naij

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DailyBookNg and Developed By Emranjega