Dole kotun laifuka ta duniya ta bincike Obasanjo, Jonathan – Inji SERAP

Kungiyar SERAP ta yi kira ga kotun hukunta laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta bincike gwamnatin tsohon shugabanni, Olusegun Obasanjo da Umaru Musa Yar'Adua da kuma Goodluck Jonathan bisa zargin da aka yiwa gwamnatunsi a kan kudin da aka ware na wutar lantarki. Kungiyar ta ce gwamnatocin da suka gabata sun yi almubazzaranci da makudan kudi mai nauyin naira tiriliyan 11 da aka ware don samar da wutar lantarki ga 'yan Nijeriya tsakanin shekarar 1999 da 2015. SERAP ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da mataimakin darektan kungiyar, Timothy Adewale, ya bayar a ranar Laraba, 16 ga watan Agusta. Kungiyar ta bukaci Fatou Bensouda, mai gabatar da kara ta kotun ICC, ta bincike zargin cin hanci da rashawa da kuma wasu manyan almubazzaranci da dukiyar al’umma wanda ya kasance laifuffuka ga 'yan Adam.