Wasu da ake zargin Yan Boko Haram ne Daga dajin sambisa sun kira shahararren dan wasan Hausar nan wato Suleman Yahaya wanda aka fi sani da BOSHO a waya tattaunawar tasu dai tazo da razanawa matukar gaske. Kiran wayar na tsawon minti biyu da sakan da sakan biyu.02:02 Wanda suka yi da Bosho din, suna magana yana maido masu Amsa, hirar ta tasu ta waya wadda aka yi recording aka dinga yadata musamman ma a kafafen Sada zumunta na whatsapp mutane da dama wadanda suka saurari Abin wasu ya basu mamaki wasu kuma sunyi dariya gami da tausayawa Dan wasan.
A cewar Wanda ake zargin da 'Yan Boko haram din ne wai sunce Bosho dai yace ya iya Had'a Atomic Bomb a cikin wani film. Hakan yasa Su kuma suka ce Zasu had'a baki da shi don kaiwa gidan Sarkin Kano Hari. Wasu suna ganin dagaske Daga 'Yan boko Haram din ne, wasu kuma masu nazarin yau da kullum suna ganin cewa 'Yan Boko Haram ba zasu kira Bosho din ta waya ba kuma har suyi Recording su yadawa duniya kawai wasu ne suka zolaye shi tare da razanashi Kasancewar Ansan jarumin ya kware wajen Barkwanci Domin su gwada basirarshi kuma susha Dariya.
wakilin Mu ya tuntubi Bosho kan gaskiyar maganar wayar tasu da 'Yan Boko Haram din sai jarumin ya ce gaskiya ba dashi akayi wayar ba, Mahassadan sa ne su ka kwaikwayi muryar sa, ga Abin da yace: Kasan Ita Rayuwa daukaka babu abinda bata Iya jawowa mutum, ni abinda na fahimta akwai wadanda suke Neman Su bata min suna a tsakanin Al'umma.
Kasan rayuwa ba yanda bata kamawa, ko ruwan alwala kake sayarwa sai an samu wasu Su burinsu suci mutuncinka, wannan maganar ba'a yi ta ba, ba'a kuma bi hanyar yinta ba. Bansan ya akai ba, kuma bansan Wanda yayi maganar ba, kuma in banda abin nan na mutane Fim din Boko Haram a kasar nan a Duniya ma Inda aka ci gaba ba'a yishi ba kuma ba zasu yishi ba, ni kawai abinda na fahimta a wannan Rayuwar kullum akwai wadanda Su burinsu suga ya za'ai suci mutuncinka. Ko Su bata dangantakarka da mutane, ni babu Wanda ya taba kirana mu hada baki dashi ayi wannan mummunan Alkaba'i. Kuma ita dai wannan Rayuwa Manzon Allah (SAW) yayi bayani mai Girma hadisi ne ingantacce. Wanda yake cewa ka fadi alheri ko kayi shiru. Amma yau wasu Al'ummar musulmi basu da hanyar samun kudi ko abinda Duniya sai ta ya za'ayi Su gurbata Rayuwar wani. Saboda haka ina kira garemu mu 'Yan wasan kwaikwayo da wadanda ke rab'e damu. Irin wannan Al'amari Billaahil azim idan kaje kiyama da irin wannan Abin a bakinka Idan manzon Allah ya karbeka Allah ya tsinan Albarka, shi ya fada mana a hadisi ingantacce ka fadi alheri ko kayi shiru.
-KANNYWOO




