Allah ya yi wa Mai alfarma Sarkin Musulmi na 18 a daular
Usmaniyya da ke Najeriya Alhaji Ibrahim Dasuki rasuwa.
Marigayi Ibrahim Dasuki ya rasu ne ranar Litinin da daddare a
wani asibiti da ke birnin Abuja yana mai shekara 93.
Wata majiya a fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato ta shaida wa
BBC cewa tuni aka fara shirye-shiryen jana'izarsa kuma ana sa ran
gudanar da ita da misalin karfe 2:00 na ranar Talata a birnin na
Sakkwato.
Alhaji Ibrahim Dasuki, wanda shi ne mahaifin tsohon mai bai wa
shugaban Najeriya shawara kan al'amuran tsaro, Kanar Sambo
Dasuki, ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki masu yawa.
SRC:- BBC



